'Yan bindiga sun kai hari kan jiragen ruwa a Naija Delta

Naija Delta
Image caption Naija Delta

Rundinar mayakan ruwan Nijeria ta ce wasu 'yan bindiga sun kai hari a kan wasu jiragen ruwan daukan kaya biyu a gabar ruwan yankin Naija Delta mai arzikin mai, har ma sun kashe ma'aikacin jigi daya.

Hakazalika, maharan sun yi garkuwa da wasu karin ma'aikatan.

Wani kakakin rundinar ya ce daya daga cikin jiragen ruwan shi ne BBC Palonia, kuma rahotannin sun ce ma'aikatan jiragen 'yan Gabashin Turai ne.

Masu aiko da rahotanni sun ce sace mutane ba wani sabon abu ba ne a yankin na Naijer Delta, kuma galibi ana sako mutanen da aka sace din, bayan an biya kudin fansar su.