'Mu 'yan Rasha ne', inji 'yan leken asiri

Michael Zottoli da Patricia Mills a kotu
Image caption Masu gabatar da kara sun ce wadanda ake zargin sun yi bayanin su 'yan Rasha ne

Masu shigar da kara a Amurka sun ce biyu daga cikin mutanen nan da ake zargi da leken asirin kasa sun bayyana cewa su 'yan kasar Rasha ne.

A cewar masu shigar da karar, bayan kama mutanen biyu a farkon wannan makon, Michael Zottoli da Patricia Mills sun amsa cewa sun lakabawa kansu sunayen jabu suna kuma amfani da takardun shaidar kasar da suka fito na jabu.

Sabanin ikirarin da suka yi cewa Michael ba'Amerike ne, ita kuma Patricia 'yar Canada ce, alal hakika mutanen biyu 'yan leken asiri ne daga Rasha, wadanda ke aiki suna kuma zaune da 'ya'yansu a wani gari da ke Virginia, yayin da suke aikewa da bayanan sirri zuwa Moscow.

A wani jawabi da suka gabatar a gaban kotu a Virginia, masu shigar da karar sun yi ikirarin cewa mutanen na aiki ne da wadansu mutanen da su ma suke fuskantar shari'a.

Sun kuma danganta mutanen da wasu akwatunan ajiya da aka gano wadanda ke cike da sababbin daloli 'yan dari-dari wadanda suka kai dala dubu dari.