Jega ya yi alkawarin gudanar da zabe ba tare da tsoro ba

Farfesa Attahiru Jega
Image caption Farfesa Attahiru Jega

Sabon shugaban hukumar zabe ta Nijeriya Farfesa Attahiru Muhammadu Jega ya bayyanawa BBC cewa zai fara aiki gadan-gadan a hukumar domin tabbatar da sahihin zabe da kuma kaucewa kura-kuran da aka yi a zabukan baya.

Yace zai gudanar da wannan aiki ba tare da tsoro ba, sannan ya kara da cewa zai gudanar da wannan aiki ba sani ba sabo.

A wata hira da ya yi da wakilinmu Ado Saleh Kankiya, Farfesa Jega ya ce daga ranar litinin hukumar za ta yi nazari akan yadda aka gudanar da ayyukan zabe a baya, sannan ya yi kira ga dukkan 'yan Nijeriya da su bayar da gudunmawa domin samun zabe mai inganci.