Kungiyar Ecowas ta dawo da Nijer a matsayin 'yar kallo

Taswirar kasashen ECOWAS/CEDAO
Image caption Taswirar kasashen ECOWAS/CEDAO

A jamhuriyar Nijer, kungiyar cigaban tattalin arzikin kasashen AFRICA ta Yamma ECOWAS /CEDEAO ta sake karbar kasar a matsayin 'yar kallo, bayan da ta dakatar da ita a 'yan watannin baya.

Kungiyar ta ce ta dauki wannan mataki ne ganin irin cigaban da gwamnatin mulkin sojan Nijer din ta yi a aikin da take na maido da kasar bisa tafarkin Dimukradiyya.

A jiya ne dai hukumar zabe mai zaman kanta ta bada ajandarta inda ta ce a ranar 3 ga watan Janairu mai zuwa ne za'a yi zaben shugaban kasa.