Kaczynski ya amince da shan kaye a zaben Poland

Poland
Image caption Poland

Dan takarar shugaban kasa a Poland, Jaroslaw Kaczynski, ya taya abokin takararsa na jam'iyyar dake mulkin kasar, Bronislaw Komorowski, murna, bayan da sakamakon farko na zaben ya nuna cewa Mr Komorowski din ne ya lashe zaben da karamin rinjaye.

Wakilin BBC a Poland ya ce sakamakon yana nufin za a samu cigaban harkokin siyasa a kasar, saboda Firaminista da shugaban kasa, dukan su sun fito ne daga jam'iyya daya.

Shugaban kasar da ya gabata, Lech Kaczynski ya rasu ne a wani hadarin jirgin sama, tare da matarsa da kuma wasu manyan jami'an gwamnatinsa da shugabannin soja.