Libya ta sakko 'yan Nijer dake zaman kaso

Shugaban Nijer Salou Djibou
Image caption Shugaban Nijer Salou Djibou

A jamhuriyar Niger wata tawaga ta farko ta 'yan kasar Nijar wadanda ake ci gaba da tsarewa a gidajen kurkukun kasar Libya suka isa Birnin Yamai.

Sakin fursunonin ya biyo bayan wata yarjejeniya ce da aka cimma tsakanin kasashen biyu, bayan kisan wasu 'yan Nijar din da aka yanke wa hukuncin kisa a Libiyan.

Hukumomin Libyan daga bisani sun amince su sako wasu 'Yan Nijar din dake gidajen kason su domin su karasa zaman sarkar da suke yi a gida.

Yayinda wadanda ke jiran shara'a su a kalla 275 za su samu tsira daga hakan a kasar Libya.

Akwai dai wasu karin fursunonin da aka yanke wa hukunci daban daban kama daga na kisa zuwa na daurin rai da rai, da yanzu haka ake kokarin warware na su batutuwan.

Wasu Karin fursunonin 'yan Niger din su kimanin 20 da tuni kotunan libiya suka yankewa hukuncin kisa, ko na daurin rai da rai a gidan yari, za su dawo a Gida a Niger domin su ci gaba da zaman wakafi a kasarsu.