China ta na son gina matatar mai a Nijeriya

Dr Goodluck Jonathan
Image caption Dr Goodluck Jonathan

Wata tawagar kamfanin mai mallakar gwamnatin kasar Sin ta fara rangadin wasu jihohin Nijeriya uku a kokarin kafa sabbin matatun mai uku a Nigeria.

A watan Mayun wannan shekara ne dai kamfanin CSCEC ya rattaba hannu kan wata yarjejeni ta dala miliyan ashirin da takwas da kamfanin mai na Nijeriya domin gina matatun man a jihohi uku na kasar.