Isra'ila ta yi sassauci kan shigar da kaya Gaza

Turkiyya
Image caption Turkiyya

Isra'ila ta tabbatar da matakan sassaucin da ta yi kan shigar da kaya Zirin Gaza, inda ta kyale a rika kai kayan masarufi zuwa yankin na Palasdinawa.

Isra'ilar ta kuma ce za a kyale a rika jigilar kayayyakin gini ta jiragen ruwa, zuwa cikin Zirin Gazan, amma cikin karkashin matakan sa ido masu tsauri.

Kungiyar gwagwarmayar Palasdinawa ta Hamas ta ce babu wani tasiri da wannan sassauci zai yi ga al'ummar Gaza, ganin cewa har yanzu akwai haramci fitar da kaya daga yankin.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da Turkiya ke cewa Isra'ilar ta fito ta nemi gafara game da mamayen da ta kaiwa jiragen ruwanta dake dauke da kayan agaji don zuwa Gaza.