Hukumar yaki da fataucin mutane ba za ta gurfanar da Yarima ba

Sanata Ahmed Sani Yarima

Hukumar yaki da fataucin mutane ta Najeriya NAPTIP, ta ce ba ta da wadatacciyar shaida ta gurfanar da Sanata Ahmed Sani yarima a gaban kotu.

Hakan a cewar hukumar ya biyo bayan kammala binciken da ta yi akan tsohon gwamnan jihar Zamfara kan zarginsa da auren yarinya 'yar shekara goma sha uku, abinda ya musanta.

Hukumar ta Naptip ta ce gurfanar da Sanatan gaban kotu ba tare da wadacciyar sheidar ba, zai zama tamkar bata kudaden al'umma ne.

Sai dai ta ce ta mika batun ga ofishin attorney janar na kasa don ya cigaba da bincike, auren da Sanata Yarima yayi ga wata 'yar kasar Masar ya janyo kace nace a ciki da wajen kasar.