Ana ganawa tsakanin Obama da Netanyahu

Obama da Netanyahu
Image caption Obama da Netanyahu

Jami'an diplomasiyya na Amurka da na Isra'ila duk suna nuna fatan ganawar da ake yi tsakanin shugaba Obama da Firaminista Netanyahu ta kasance mai armashi.

Dangantaka tsakanin Isra'ila da Amurka ta shiga cikin wani mawuyacin hali a 'yan watannin baya.

Ta wani bangaren hakan na faruwa ne a sakamakon bambancin manufofi, akwai kuma batun muhimmin sauyin da aka samu dangane da dangantaka tsakanin kasashen biyu.