An karrama 'yan wasan Ghana

Ghana ta sha kashi ne a hannun Uruguay
Image caption Ghana ta taka rawar gani sosai a gasar ta bana

Al'ummar Ghana sun yiwa 'yan wasan Black Stars na kasar gagarumar tarba a lokacin da suka isa filin saukar jiragen sama na Accra a ranar Litinin, bayan sun dawo daga gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya.

Dubun dubatar 'yan kasar ne dai suka hallara a wajen domin yi musu maraba cikin har da ministoci da manyan jami'an gomnati.

Wakilin BBC a Accra, Iddi Ali wanda na cikin wadanda suka gane ma idanunsu saukar 'yan wasan, yace jama'ar gari da jami'an gwamnati sun nana farin ciki kan rawar da 'ya wasan suka taka.

Tun kafin 'yan wasan su sauka ne dai akayi ta kade-kade da raye-raye na yin marhabin da su.

Fitowar 'yan wasan daga cikin jirgin saman ke da wuya sai duk wurin ya rude da sowa da bushe bushen algaitar nan ta vuvuzela.

Image caption Wasu magoya bayan Ghana a Afrika ta Kudu

An dai yi ta kiran sunayen 'yan wasan guda guda a yayin da suke takawa don zuwa gaida ministoci da manyan jami'an gwamnatin dake jiransu.

A jawabin da yayi a wajen Mista Alex Segbefia, mataikain babban jami'in dake kula da fadar shugaban kasa, ya yabama 'yan wasan kan namijin kokarin da yace sun yi. Yace kun samu cikin farin ciki da alfahari. Zan tabbatar muku da cewa zuciyar al'ummar Ghana baki daya fari take game da ku, musamman Asamoah Gyan, bai kamata a damu da abin da ya cika da shi ba.

"Kamar wani karin magana ne dake cewa wanda ke zuwa maka rafi wata rana shi zai fasa maka tulu," in ji Alex Segbefia.

Kaptin din 'yan wasan wato Stephen Appiah ya godema al'ummar kasar kan karfin gwuiwar da yace sun basu. "A madadin 'yan wasan Black Stars ina tabbatar muku da cewa munyi iyakar kokarin mu don kafa ma kasar mu da sauran kasashen Afrika tarihi to amma rana ce ta baci. Muna kara gode muku kan gagarimin goyan bayan da kuka bamu," in ji Appiah. Daga bisani 'yan wasan sun garzaya cikin gari kan wasu manyan titunan birnin gabanin su gana da shugaba John Atta Mills a fadarsa dake Accra.

'Yan wasan Black Stars na Ghana ne suka kai zagayen dab dana kusa da karshe cikin kasashen Afrika da suka je gasar.

Kasar Uruguay ce ta fitar da su a wasan dab dana kusa dana karshe cikin wani yanayi mai rudarwa.