Gwamnatin Kenya zata tattauna dokar karin kudaden 'yan majalisa

Shugaba Mwai Kibaki na Kenya
Image caption Shugaba Mwai Kibaki zai jagoranci wata tattauna da 'yan majalisar zartarwarsa domin duba dokar karin kudade ga 'yan majalisar kasar

A yau ne shugaba Mwai Kibaki na Kenya zai jagoranci wani zama na musamman na majalisar zartarwar kasar domin daukar mataki kan dokar da 'yan majalisar dokokin Kenyan su ka yi da sanyasu cikin jerin yan siyasar da aka fi biya da tsada a duniya.

Idan gwamnatin ta amince da dokar, albashin yan majalisar da alawus-alawus zai kai dalar Amurka dubu dari da hamsin a kowace shekara.

Sai dai jami'an gwamnatin ciki har da firaminista Raila Odinga sun baiyana rashin amincewarsu da dokar.

Kungiyoyin kwadago kuma sun yi barazanar shiga yajin aikin mako guda idan har dokar ta tabbata.