An sabunta: 8 ga Yuli, 2010 - An wallafa a 12:52 GMT

Faransa na gab da hana sanya Niqabi

Hjabin burqa

Wata mace musulma sanye da hijabin burqa na sayayya awani kanti a Faransa

Majalisar dokokin Faransa ta fara tattaunawa kan dokar hana mata sanya burqa ko kuma niqabin musulunci a bainar jama'a dama cikin gidajen su.

Za a kada kuri'a a kan daftarin dokar a mako mai zuwa kafin cikakkiyar kuri'ar da majalisar dattawa za ta kada a watan Satumba.

Idan aka amince da dokar to za a hana amfani da hijabin a cikin sirri da kuma bainar jama'a.

Masu adawa da shirin sun ce gwamnati na san takurawa musulmai mata da ke sanya hijabin mai rufe jiki ne kawai, wadanda adadinsu bai wuce 2,000, kamar yadda ma'aikatar cikin gida ta bayyana.

Wakilin BBC a birnin Paris Christian Fraser, yace dokar na samun goyon bayan jama'ar kasar, sai dai akwai masu adawa da ita.

Jam'iyyar adawa ta 'yan burguzu wacce ke son takaita haramcin kan wuraren da jama'a ke halatta, za ta kauracewa kada kuri'ar.

Martanin malaman addinin musulunci

Amma acewar Ustaz Aminu Ibrahim Daurawa wani malamin addinin Musulunci a Kano, wannan matakin bai dace da tsarin da aka san Faransa da shi ba tun asali.

A hirar sa da wakilin BBC Naziru Mika'il ta wayar tarho, malamin yace musulman na Faransa nada damar daukar matakai da dama domin neman 'yan cinsu.

Kusan tun 1971 Faransa ta fara kiran da asamarwa da dan adam 'yan cin rayuwa wanda ya hada da addini na siyasa da kuma tsaro, kuma wannan shi ne abin da addinin musulunci ya tanada.

"Don haka akwai mamaki idan yanzu ta zo tace ta hana mata yin shigar da addininsu ya tabbatar musu," a cewar malamin.

Idan har Faransa ta dauki wannan mataki, kuma sauran kasashen musulmai su ma suka hana bayyana alamun addinin da ba nasu ba, to duniyar ma ba za ta zaunu ba

In ji Ustaz Daurawa

"Matakin da musulman Faransa za su iya dauka zai danganta ne da kasancewar su 'yan kasar, ko kuma baki mazauna kasar, ko kuma wadanda suka je kasar domin karatu."

Don haka za su duba duk irin wadannan abubuwa kafin su yanke hukunci.

Ya kara da cewa za su yi shawara domin sanin irin matakin da ya kamata su dauka, wanda zai iya hadawa da rubuta koke zuwa majalisar dinkin duniya da sauran kasashen musulmai.

"Idan har Faransa ta dauki wannan mataki, kuma sauran kasashen musulmai su ma suka hana bayyana alamun addinin da ba nasu ba, to duniyar ma ba za ta zaunu ba," in ji Ustaz Daurawa

Ustaz Aminu Daurawa ya kuma ce, halin da musulmin suka samu kan su a ciki, shi zai taimaka wajen irin matakin da za su dauka.

"Tunda doka ce za a yi bawai larura bace musulmi ya samu kansa a ciki, kamar ta rashin tufafi ko kuma kafin ya shiga kasar ya san ba a yin musulunci".

"Ana yawo da kuros da sauran alamu na addinai, don haka ba maganar wani 'yan cin dan adam, ko raba addini da al'amuran rayuwa, kuma wajibi ne akyale kowa ya yi addininsa," a cewar Usataz Aminu Daurawa.

Tuni dai babbar majalisar kasa da ke baiwa gwamnati shawara tayi gargadin cewa matakin ka iya sabawa tsarin mulkin kasar, amma alamu na nuna cewa za a amince da dokar, wacce za ta hana amfani da hijabin a cikin sirri da kuma bainar jama'a.

Za a ci tarar duk wacce aka samu ta sanya hijabin tarar Yuro 150, da kuma tsattsauran mataki kan namijin da aka samu da laifin umartar matar sa yin amfani da hijabin a cikin gida, wanda ka iya hadawa da zaman gidan yari.

Sai dai yiwuwar wannan ka iya zamowa wani abin cece-kuce nan da mako mai zuwa ganin mahimmancinsa ga al'umar musulmai.

Tattaunawar za ta maida hankali ne kan irin musuluncin da Faransa ke son ganin anyi da kuma makomar musulmai miliyan shidan da ke zaune a kasar.

A dawa da hijabin dai na kara karuwa ne saboda ginin wani katafaren masallaci da musulmi ke yi a kasar, wanda ke kara nuna zaman dirshan din da addinin musulunci ke yi a tsakanin al'ummar kasar ta Faransa.

Kuma a kasar da jama'a ke da akidar raba addini da al'amuran mulki da kuma adawa da al'adu da dama, hakan wani kalubale ne ga akidar da jama'ar kasar suka yi imani da ita.

Rabe-raben Niqabin da mata ke amfani da shi

 • Abaya
  Ana amfani da kalmar Hijab ne, wacce ta samo asali daga Larabci, domin siffanta Hijabin da mata ke sawa. Anahiyar Turai matan kan rufe kansu da jikinsu amma banda fuskokinsu.
 • Niqab
  Niqab kan rufe fuska sannan ya bar gurbin ido a bude. Sai dai akan yi amfani da shi tare da abin rufe ido na daban koma da dan kwali na musamman.
 • Niqabi Mai Raga
  Burka-wato Niqabi mai riga, itace mafi kyawun shiga ta musulunci, tana rufe baki dayan jiki da fuska, tare da barin kofa 'yar kadan.
 • Mayafi
  Shayla-wato Mayafi, yana da tsayi kuma ana amfani da shi sosai a kasashen Larabawa. Ana rataya shi tun daga kafada zuwa gadon baya.
 • Shari
  Chador-wato Shari, matan Iran ne suka fi amfani shi idan suna waje, yana rufe jiki gaba daya. A mafi yawan lokuta yana dauke da karamin mayafi.

Sauran kasashen Turai

Sauran kasashen Turai kamar su Italiya da Belgium da Burtaniya da Jamus da Holland duka sun yi tsaiko ga irin wannan tufafi da mata musulmi ke sanyawa.

Su ma kasashe irnsu Turkiyya tuntuni suka dakatar da amfani da Niqabi a bainar jama'a.

Yayinda kasashe irinsu Austria da Switzerland suka yi alkawarin dakatar da amfani da shi, muddum dai adadin matan da ke amfani shi suka karu.

BBC navigation

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.