An hallaka mutane akalla talatin a Iraki

Hubbaren Imam Moussa Al-Kadhim dake Bagadaza
Image caption 'Yan Shiar da aka kai wa hari suna ziyartar hubbaren Imam Moussa Al-Kadhim ne dake Bagadaza

Jami'an tsaro a birnin Bagadaza na Iraki sun ce, wasu hare-haren bam da aka kaiwa 'yan Shi'a masu ziyarar ibada, sun janyo hallakar mutane fiye da talatin, sannan wasu fiye da dari sun sami raunuka.

Dimbin masu ziyarar ibadar na kan hanyarsu ce ta zuwa hubbaren Imamu Moussa Al-Kadhim dake birnin Bagadaza.

An kai hare-haren ne a daidai lokacin da Amirka ke gaggauta janye dakarunta daga Irakin.

Ma'aikatar tsaron Amirka na son ganin dukan sojoji masu zuwa fagen daga, sun fice daga Irakin nan da karshen watan gobe.