Sarauniya na son tabbatar mulki nagari

Sarauniyar Ingila,Queen Elizabeth ta biyu
Image caption Sarauniyar Ingila ta yi jawabi ga taron Majalisar Dinkin Duniya

Sarauniyar Ingila, Queen Elizabeth ta biyu ta jaddada muhimmancin samun shugabanci na gari da zai tabbatar da samun dawwamammen zaman lafiya a duniya.

A jawabinta na farko a matsayin shugabar kungiyar kasashe rainon Ingila wato Common Wealth ga Majalisar dinkin Duniya na fiye da shekaru hamsin, ta kuma yi kira ga kasashen duniya da su hada kai wajen tunkarar sabbin kalubale da suka hada da yaki da ta'addanci da matsalar sauyin yanayi.

Sarauniyar ta Ingila ta ce ta ga gagarumin sauyi a Majalisar Dinkin Duniya tun bayan data ziyarci Majalisar a shekarar dubu da dari tara da hamsin da bakwai.

Ta kara da cewa yana da kyau a samu ingantacciyar hanyar da zata tabbatar da yalwatuwar kasashen duniya.