Cuba za ta saki fursunoni 52

Shugaban kasar Cuba,Raul Castro
Image caption Kasar Cuba ta amince ta saki fursunonin siyasa

Gwamnatin kasar Cuba ta amince ta saki 52 daga cikin Fursunonin siyasar da ta ke tsare da su.

Za a saki fursunonin ne bayan da suka shafe shekaru da dama a tsare a kasar ta Cuba.

Sanarwar sakin fursunonin na zuwa ne bayan wata ganawa tsakanin shugaban kasar Cuban Raul Castro,da ministan harkokin wajen Spain,Miguel Angel Moratinos,da kuma shugaban cocin Katolika ta kasar Cardinal Ortega

Fursunonin na daga cikin ragowar mambobin wata kungiyar manyan 'yan adawa guda 72 wadanda gwamnatin kasar ta farwa a shekarar 2003.

Hakan dai na nufin wadannan sune mafi yawan fursunoni da kasar ke saki cikin shekaru da dama.