Taron koli na kungiyar D8

Shugaba Ahmadinejad na Iran
Image caption Shugaba Ahmadinejad na Iran na halartar taron na Abuja

Shugabannin kasashen nan takwas masu tasowa, wato D8, na taro a Abuja, Najeriya.

An dai soma taron ne bayan kasar Malaysia ta mika wa Najeriya shugabancin wannan kungiya, wadda mambobinta suke da dimbin al'ummar Musulmi.

Shugabannin kasashen takwas za su maida hankali ne ga batutuwan da suka hada da kara yawan hada-hadar kasuwanci tsakaninsu ya zuwa dala tiriliyan 1.7 nan da shekara ta 2012.

Hakazali ana sa ran taron zai bada goyon baya ga amfani da makamashin nukiliya don ayyukan da suka shafi farar hula, wanda hakan tamkar goyon baya a boye ne ga Iran a takaddamar da take yi da Amurka a kan shirinta na nukiliya.