Ana zargin dan sanda da sace mutane a Najeriya

'yan sanda na sunturi a Najeriya
Image caption An dade ana zargin 'yan sandan Najeriya da hada kai da masu laifi

Rundunar 'yan sandan Najeriya na gudanar da bincike kan wani babban jami'in gundumar 'yan sanda (wato DPO) da ke birnin Enugu, bisa zargin hannu a jerin wasu sace-sacen jama'a ana garkuwa da su a jihar Enugu.

To sai dai yayin da binciken ke gudana, hedikwatar rundunar 'yan sandan ta ce ba ta kai ga samunsa da wani laifi ba tukun. Jami'in hulda da jama'a na hedikwatar rundunar 'yan sandan Najeriya, Emmanuel Ojukuwu, ya shaidawa wakilin BBC a Enugu Abdussalam Ibrahim Ahamed cewa:

"Binciken da ake gudanarwa ya biyo bayan wata takardar koke ce da muka samu, wadda ke zargin babban jami'in gundumar 'yan sanda na Awkunanaw a nan birnin Enugu.

Da babban Sufuritendan 'yan sanda Sam Chukwu, cewa yana da hannu a laifuffukan da suka shafi sace mutane ana garkuwa da su.

Yace a wani bangare na nauyin da ke kanmu cewa, mu tabbatar jami'an da ke aiki a karkashin rundunar mu, sun kasance masu kyakkyawar halayya, da aiki bisa gaskiya da doka, sai aka gayyato wannan jami'in zuwa hedikwata, inda ake gudanar da bincike kansa.

An dade ana zargin shi wannan jami'in 'yan sanda a kan taimaka wa masu sace mutane suna garkuwa da su, kuma yana cin gajiyar abin da ake samu daga wannan ta'asa.

Amma sai dai magana da yawun 'yansandan yace kawo yanzu, babu wata kwakkwarar shaida wadda ke nuna cewa, wannan mutum yana da hannu a wadannan laifuffuka da ake zarginsa da su.

Sai dai kuma Mista Emmanuel Ojukwu ya ce, bincike game da danyar magana irin wannan, wani abu ne da akan bari bude har sai an dangana da karshen al'amarin:

"Za mu ci gaba da bin diddigin wannan batu, don mu tabbattar cewa, muddin yana da hannu a wannan lamari an hukunta shi kamara yadda doka ta tanada. Idan kuma ba shi da laifi za a yi masa adalci," in ji Ojukwu.

Ganin cewa an dade ana zargin rufa-rufa a wannan batu, ganin yadda abin ka iya bata sunan 'yan sandan kasar, amma sai jami'in 'yan sandan yace: Hukumar 'yan sanda ba ta boye jami'anta da suka aikata laifuffuka. Don haka babu wata rufa-rufa kamar yadda ake hasashe.

An dade ana zargin cewa, wasu bata-gari a cikin 'yan sanda kan taimaka ko ma sukan aikata miyagun laifuffuka da kansu a Najeriya.

Sai dai kuma rundunar 'yan sandan kasar tana ta bayani cewa, tana yin iya bakin kokarinta wajen kawar da ire-iren wadannan baragurbi a duk lokacin da aka bankado su.