'Yan kasuwar motoci sun koka a Nijar

Taswirar jamhuriyar Nijar
Bayanan hoto,

'Yan kasuwar Nijar sun koka kan yadda ake karbe kudadensu

A Jamhuriyar Nijar, 'yan kasuwa masu sayo motocin gwanjo daga tashoshin ruwan Kotono,da Lome na kokawa da matsalar karbar kudade a hannunsu da wasu jami'ai ke yi a kan hanyoyinsu na zuwa jamhuriyar Nijar.

'Yan kasuwar sun yi kira ga gwamnatoci da kuma jami'an shige-da-fice da su gargadi masu karbar musu kudaden,inda suka yi tur da al'amarin.

'Yan kasuwar dai da suka hada da 'yan kasar Nijar da Najeriya sun ce sun dade suna fuskantar irin wannan hali.

Al'amarin karbar kudade ga jami'an tsaro a wurin 'yan kasuwar na bata sunayen kasashen.