Rasha da Amirka sun yi musayar fursunoni

Jiragen da suka dauko jami'an leken asirin
Image caption Musayar fursunonin ita ce mafi girma tun bayan yakin cacar baki

Amirka da Rasha sun yi musayar fursunoni mafi girma tun bayan yakin cacar baki na duniya.

Jiragen sama 2- daya na Rasha, gudan kuma na Amurka- sun jera da juna a kan hanyar sauka da tashin jiragen sama ta filin jiragen sama na Vienna na tsawon kusan mintuna 55 yayin da aka yi musayar jami'an leken asirin Rashar nan goma da aka kama a Amurka da mutane 4 da aka samu da laifin leken asiri a Rasha.

Musayar jami'an leken asiri tsakanin Amurka da Rasha ya sake jaddada irin hayaniyar cacar bakin da har yanzu take kankane dangantaka tsakanin Amirka da Rasha.