Sama da mutane miliyan daya sun yi maci a birnin Barcelona

Catalonia
Image caption Catalonia

Mutane fiye da miliyan daya sun yi maci a birnin Barcelona na Spain don nuna goyon baya ga batun samun 'yancin cin gashinn kai na yankin Catalonia.

An gudanar da zanga-zangar ne, bayan wani hukunci da kotun tsarin mulkin Spain din ta yanke, wanda ya ce babu wata hujja ta fuskar shari'a da za a ba Catalonia din matsayin wata kasa, kuma bai kamata harshen Catalan ya maye gurbin harshen Spanish a yankin ba.

Shugaban yankin na Catalonia, Jose Montilla ya ce hukuncin kotun zai janyo wasu sababbin matsaloli.

'Yan adawa na masu matsakaicin ra'ayi na Peoples party ne dai suka shigar da karar da ta kai ga yanke hukuncin.