Bentacourt ta nemi diyyar daga kasar Colombia

Shugaba Juan Manuel Santos
Image caption Shugaba Juan Manuel Santos ya ce bukatar ta Mis Bentacourt alama ce ta rashin godiyar Allah

'Yar siyasar nan ta kasar Colombia wadda aka yi garkuwa da ita, Ingrid Betancourt, ta nemi gwamnatin kasar ta biyata diyyar shekarun da ta kwashe a hannun 'yan tawaye.

Mis Bentacourt dai ta kasance cikin matan da suka shahara a duniya bayan kubutar da ita da sojoji suka yi tare da wadansu mutanen goma sha-biyar da 'yan tawayen FARC suka yi garkuwa da su.

An dai yabawa Mis Betancourt saboda kamun kan da ta nuna a lokacin, musamman ma yadda ta yi mu'amala da kafofin yada labarai.

To amma yanzu tana shan kakkausar suka bayan ta bukaci gwamnatin kasar ta Colombia ta biya ta diyyar dala miliyan shida da dubu dari takwas a matsayin fansar zaman da ta yi na shekaru shida a hannun 'yan tawaye.

An dai sace Mis Bentacourt ne a shekarar 2002 lokacin da ta je yankin da 'yan tawayen ke da karfi a yakin neman zaben da ta yi na zama shugabar kasar, duk kuwa da gargadin da sojojin kasar suka yi mata cewa hakan na da hadarin gaske.

Ma'aikatar tsaron Colombia ta bayyana takaici da mamakinta dangane da wannan bukata.

Shi kuwa shugaban kasar, Juan Manuel Santos, wanda shi ma aka taba yin garkuwa da shi har tsawon wata takwas, cewa ya yi bukatar alama ce ta rashin godiyar Allah.