Kamfanin BP na yunkurin karshe na hana malalar mai

Malalar mai a tekun Mexico
Image caption Malalar mai a tekun Mexico

Kamfanin mai na BP ya fara yunkurinsa na karshe na dakatar da matsalar nan ta malalar mai a tekun Mexico.

Yanzu haka kamfanin na amfani ne da wasu na'urori don kawar da murfin da aka rufe rijiyar da ta fashe, don maye gurbinsa da wani sabon murfin, wanda ya kamata ya hana duk wata tsiyayar mai cikin teku.

Idan wannan aiki ya yi nasara, kamfanin zai dakatar da malamar man daga mako mai zuwa, amma idan aka cire murfin na farko, to man zai cigaba da malala sai lokacin da aka yi nasarar rufe rijiyar da sabon murfin.

Sai dai ana ganin cewa wannan matakin wucin gadi ne, saboda kamfanin na BP na bukatar haka wasu riyoji biyu a karkashin tekun, don toshe rijiyar baki dayan ta.