Jirgin ruwan kai agaji Gaza ya nufi Masar

Binyamin Netanyahu
Image caption Binyamin Netanyahu

Jami'ai a Isra'ila da Girka sun ce wani jirgin ruwa dauke da kayan agaji zuwa Gaza, yanzu ya doshi Masar, bayan yunkurin diplomasiyyar da gwamnatin Isra'ila ta yi.

Jami'an sun ce jirgin ruwan, wanda wata kungiyar agajin kasar Libya ta yi shatarsa, ya taso ne daga Girka zuwa tashar jiragen ruwan El Arish dake Masar, wadda ke kusa da Gaza.

Sai dai shugaban kungiyar agajin ta Libya, Youssef Sawwan ya fadawa BBC cewa jirgin ruwan ba zai canza alkibilarsa ba, kuma zai je tashar jiragen ruwan Gaza.

Isra'ila dai ta ce shirin tura wani jirin ruwan zuwa Gaza, wata takala ce, saboda a kwanan nan ta sassauta killacewar da ta yiwa Gaza ta hanyar bada damar shiga yankin da karin kayyaki.