Isra'ila ta hana jirgin ruwa kai agaji zuwa Gaza

Ministan harkokin wajen Isra'ila
Image caption Ministan harkokin wajen Isra'ila

Ministan harkokin wajen Isra'ila, Avigdor Lieberman ya ce kokarin diplomasiyya ya taimaka wajen hana wani jirgin ruwa dauke da kayan agaji, isa Zirin Gaza, wanda Isra'ila ta killace.

Wata kungiyar agaji da dan shugaban Libyan, Kanar Gadhafi ke shugabanta ce dai ta so ta tura jirgin ruwan na kasar Moldova, daga Girka zuwa Gaza; amma Mr Lieberman ya ce a sakamakon tattaunawar da ya yi da takwarorin aikinsa na Girka da Moldova, yanzu jirgin ruwan zai tsaya ne a kasar Masar.

Wakilin BBC ya ce Isra'ila ta ce shirin na tura wani jirin ruwan zuwa Gaza, wata takala ce, saboda a kwanan nan ta sassauta killacewar da ta yiwa Gaza ta hanyar bada damar shiga yankin da karin kayyaki.