Shugabannin Sudan sun kaddamar da shawarwari

Shugaban Sudan Omar Albashir
Image caption Shugaban Sudan Omar Albashir

Shugabannin Arewaci da Kudancin Sudan sun kaddamar da wasu shawarawri kan yadda za su tunkari sakamakon kuri'ar raba gardamar da za a yi a badi kan batun 'yancin kan kudancin kasar.

A wasu jerin taruruka da za su yi, bangarorin biyu za su tattauna batutuwa da dama da suka hada da batun zama dan kasa da iyakoki da kuma rabon arzikin kasa.

Kuri'ar raba gardamar dai tana a matsayin wani bangare ne na shirin zaman lafiyar kasar, wanda aka sanya wa hannu shekaru biyar da suka wuce, wanda kuma ya kawo karshen yakin basasar da aka shafe shekaru da dama ana yi tsakanin Arewaci da Kudancin kasar ta Sudan.