Ana bikin tunawa da kisan gillar da Sabiyawa su ka yiwa musulmin Bosnia

Bosnia
Image caption Bosnia

Ana gudanar da bukukuwa a Bosnia Hercegovina na tinawa da kisan gillar da sojojin Sabiya suka yiwa wasu musulmi mazaje da samari su fiye da dubu bakwai a Srebrenica, shekaru 15 da suka wuce.

Ana daukan kisan dai a matsayin ta'asa mafi muni da aka tafka a Turai, tun bayan yakin duniya na biyu.

Daruruwan jama'a ne dai suka halarci jana'izar mamata fiye da dari bakwai da aka tantance su a kwanan nan, a makabartar Potocari.

A wurin jana'izar, shugabannin kasashe sun yi kiran sassantawa, da kuma a gurfanar da wadanda ke da hannu a kisan a gaban shari'a.

Shugabannin duka kasashen da ke cikin tsohuwar Tarayyar Yugoslavia, ciki har da shugaban Serbiya, Boris Tadic, sun halarci jana'izar.