Firaministan Japan ya ce ba shi da niyyar yin murabus

Japan
Image caption Japan

Firaministan Japan Naoto Kan ya ce ba shi da niyyar yin murabis, duk da kayen da gwamnatinsa ta sha zaben 'yan majalisar dokokin kasar.

Sakamakon farko na zaben ya nuna cewa kawancen jam'iyyun dake mulki sun rasa rinjayen da suke da shi a majalisar Dattawan kasar.

Hasashen da aka yi ya ba jam'iyyar DPJ ta Mr Kan kusan kujeru 47, amma duka sauran kananan jam'iyyu da suka yi da ita, ba su samu koda kujera daya ba.

A wani taron manema labarai, Mr Kan ya nemi afuwa.

A bara ne dai jam'iyyar ta DPJ ta hau kan karagar mulki, tare da yiwa jamaa alkawarin kawo wasu muhimman sauye-sauye.

Sai dai farin jinin ta ya ragu ainun, saboda irin abubuwan rashin gaskiyar da aka tafka a fannin kudi da kuma raunin shugabancin da jam'iyyar ta nuna.