Hama Amadou ya ce zai yi takara a Nijar

Taswirar Jamhuriyar Nijar
Image caption Tsohon Firayim Minista Hama Amadou ya ce zai yi takarar shugaban kasar Nijar badi

Tsohon firayim ministan Jamhuriyar Nijar, Malam Hama Amadou, ya ce zai shiga takarar neman kujerar shugaban kasa a zaben badi.

Malam Hama Amadou ya fadi haka ne a jawabinsa na farko bayan zabensa a matsayin shugaban jam'iyyar MODEN-Lumana Africa, a karshen babban taron jam'iyyar.

Ya kuma shaidawa BBC cewa dukkan zarge-zargen da aka yi masa a baya ba gaskiya ba ne.

ā€œDuk abuwan da aka kulla mini karya ne; yanzu [a] bincike[n da] ake yi kun taba jin suna na?ā€

Malam Hama Amadou ya ce jam'iyyarsa na da kyawawan manufofin da za su ciyar da Nijar din gaba, wadanda suka hada da samar da makamashin nukliya da kuma samar da ayyukan yi ga matasa.