Mutanen Japan na zaben 'yan majalisa

Firayim Minista Naoto Kan na Japan
Image caption Zaben gwajin farin jinin jam'iyyar DPJ ta Firayim Minista Naoto Kan ne

Da sanyin safiya al'ummar kasar Japan suka fara fita don kada kuri'a a zaben Majalisar Dattawa.

Ko da yake a ma'aunin siyasar kasar zaben ba wani nauyi ne da shi can can ba, kasancewar rabin kujerun majalisar ne za a cike, wannan wani zakaran gwajin dafi ne ga irin farin jinin da jam'iyyar Democratic Party of Japan (DPJ), ta masu matsakaicin ra'ayi, ta ke da shi.

Bara ne dai jam'iyyar ta dare gadon mulki tare da alkawarin kawo sauyi bayan shekaru hamsin na mulkin masu ra'ayin mazan jiya.

Hakazalika, zaben wata dama ce ga Japanawa su nuna irin amincewarsu da Naoto Kan, wanda ya dare kujerar firayim minista a watan Yuni bayan Yukio Hatoyama ya yi murabus ba zato ba tsammani.

Da fari dai kuri'un jin ra'ayin jama'a sun nuna cewa Mista Kan na da farin jini sosai, to amma tauraruwarsa ta fara dusashewa bayan ya bayar da shawarar cewa a rubanya haraji don ceto kasar daga fadawa tarkon dimbin bashin da ka iya durkusar da tattalin arzikinta.

A 'yan kwanakin nan dai ya dan sauya matsayinsa, yana mai cewa ko za a kara haraji ma sai bayan wasu shekaru.

In dai jam'iyyar DPJ ta kasa yin katabus a wannan zabe to wajibi ne Mista Kan ya fadada gwamnatinsa ta hadin gwiwa ko kuma ya fuskanci turjiya a majalisa, al'amarin da ka iya raunata shugabancinsa na jam'iyyar.