Gwamnati za ta rasa rinjaye a majalisar dattijai a zaben Japan

Zabe a Japan
Image caption Zabe a Japan

Sakamakon farko na zaben 'yan majalisar dokokin da aka yi a Japan ya nuna cewa mai yiwa gwamnati ta rasa rinjayen da take da shi a majalisar Dattawa.

Sakamakon farkon ya nuna cewa jam'iyyar Democratic party of Japan, DPJ da sauran kananan jam'iyyu da suke kawance da ita, sun rasa kujeru da dama:

Wakilin BBC ya ce akwai yiwuwar Firaminista Nato Kan ya nemi yin kawance da wasu kananan jam'iyyu don kada a fuskanci wani yanayi mai wuyar sha'ani a majalisar.

A bara ne dai jam'iyyar ta DPJ ta hau kan karagar mulki, tare da yiwa jama'a alkawarin kawo wasu muhimman sauye-sauye.

Sai dai farin jinin jam'iyyar ya ragu ainun, saboda irin abubuwan rashin gaskiyar da aka tafka a fannin kudi da kuma raunin shugabancin da jam'iyyar ta nuna.