An sako mataimakin shugaban majalisar dokokin Liberia

Liberia
Image caption Liberia

An sako mataimakin shugaban majalisar dokokin Liberia, Tokbah Mulbah, bayan da aka yi masa daurin talala na dan gajeren lokaci bisa zargin cewa ya bada umarni aka yiwa wani dan sanda duka.

'Yan sanda sun fice daga gidan Mr Mulbah dake Monrovia, babban birnin kasar, bayan da ya yi musu bayani a rubuce kan abun da ya faru.

Ba a dai tuhume shi da wani laifi ba.

Tun farko dai jami'an tsaro sun ce an daki dan sandan ne har ya suma, bayan da ya yi yunkurin kwace daya daga cikin motocin Mr Mulbah.

Mr Mulbah dai ya musanta zargin.