Ana takaddama kan rabon filaye a Maradi

Nijer
Image caption Nijer

A Jamhuriyar Nijer har yanzu dai tsugune ba ta kare ba a takaddamar da ake yi a garin Tasawa na jihar Maradi tsakanin ofishin magajin gari da wasu al'ummar garin dangane da batun mallakar wasu filaye.

Sama da filaye dubu daya ne dai ake sa ran ofishin magajin garin zai kwace daga hannun jama'a bayan da ofishin ya gano cewa an mallake su ba bisa ka'ida ba.

Ranar Juma'ar da ta wuce dai, daruruwan mazauna garin na Tasawa sun yi zanga-zanga don nuna bacin ransu da matakin da magajin garin ya dauka.