Wani matashi ya yi kokarin hallaka Sarkin Kano

Taswirar Nijeria
Image caption Taswirar Nijeria

Rundunar 'yan sandan jihar Kano a Nijeria ta ce tana rike da wani matsahi mai shekaru 19 da wani dattijio mai shekaru 65 bisa zarginsu da shirin kashe Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero ranar Juma'ar da ta gabata.

Matashin mai suna Usman Musa ana zarginsa ne da laifin daukar wani abu da ya yi kama da bindigar hannu, inda bayan an ida sallar Juma'a ya bayyana cewa ya zo ne da nufin kashe sarki, kuma ana zargin cewa dattijon Alhaji Abubakar Hamidu Batakaye wanda shi ma a lokacin yana masallacin, shi ne ya sa shi.

Sai dai Dattijon ya musanta zargin, inda ya ce sama da shekaru goma da ma a wannan masallacin yake sallar juma'a.