Spain ta lashe kofin duniya

Spain da Holland
Image caption Spain da Holland

Kasar Spain ta lashe gasar cin kofin kwallon kafa na duniya a Afrika ta Kudu inda ta lallasa Holland da ci daya mai ban haushi.

Gasar cin kofin duniyar dai ita ce ta farko da aka yi a nahiyar Afrika.

Spain din dai ta sami nasara ne a karin lokaci bayan an kammalla mintina casa'in na farko.

Kasar Spain yanzu ta kafa tarihi inda ta zama kasa ta takwas a cikin jerin kasashen da suka taba cin gasar.

Kasashen dai sune, Uruguay da Jamus da Brazil da Ingila da Argentina da Italiya da Faransa, yayin da Spain din ta zama kasa ta takwas.

Masu lura da al'amuran yau da kullum na ganin Spain din ta cancanci yin nasara a gasar musamman ganin irin kwallon da ake takawa a kasar, sannan ita ce take rike da kambun nahiyar Turai.

Kasar Hooland din ita ma ta yi kokari sosai a wasan, inda ta sami dama amma ba ta iya amfani da ita ba.

Wannan shi ne karo na uku da Holland ta kai zagayen karshe amma ba ta iya daukar kofin ba.