'Yan bindiga sun tsallaka Pakistan daga Afghanistan

Ministan harkokin cikin gida na Pakistan Rahman Malik ya ce wasu 'yan bindiga da suka tsallaka kan iyaka suka shiga Pakistan daga Afghanistan su ne ke da alhakin kai wani hari a yankin kabilar Mohmand, inda aka tabbatar da mutuwar mutane dari da bakwai.

Harin, wanda aka kai ranar Juma'a shi ne mafi muni a Pakistan bana, kuma Mr Malik ya ce matakan da Afghanistan da NATO ke dauka ba su wadatar ba, wajen hana kutsen da ake yi ta kan iyaka.