Kamfanin mai na BP ya ce yana samun nasara

Tambarin kamfanin mai na BP
Image caption Kamfanin BP ya ce yana samun nasara a yunkurin hana tsiyayar mai a Tekun Mexico

Kamfanin mai na Birtaniya, BP, ya ce yana samun nasara a yunkurinsa na baya bayan nan na rage man da ke kwarara daga wani bututu a karkashin Tekun Mexico da ya fashe.

Manyan jamiā€™an kamfanin na BP sun ce sabon marufin da aka sanya a bututun da ya fashe, wanda ya kamata a ce man da ke tsiyaya yana kwarara cikinsa, za a iya kammala aikinsa a ranar Laraba.

Mai da yawan gaske ya kwarara cikin teku, tun lokacinda wani naurar hakar mai ya yi bindiga ya nutse a watan Afrilu.

Uwar gidan shugaban kasar Amurka, Michelle Obama, na shirin kai ziyara don ganin irin barnar da tsiyayar man ta haifar; ana kuma sa ran za ta gana da iyalan da abin ya shafa.