An fara zirga zirgar jirgin kasa a jahar Kano

Jirgin kasa
Image caption Jirgin kasa

Hukumar sufurin jiragen kasa ta Najeriya ta fara wani yunkurin farfado da sufurin a dukan fadin kasar, inda a Kano aka fara wata zirga zirgar jirgin kasa daga cikin birnin Kanon, zuwa kauyen Challawa mai nisan kilomita 19.

Hukumar ta samar da wani sabon kan jirgi mai aiki da tarago tara, wadanda aka yiwa kwaskwarima domin gudanar da sufurin.

Jirgin na tsayawa ne a tashoshi takwas. Jama'a da dama a Kanon, musamman masu bin hanyoyin da jirgin yake bi, sun bayyana wa BBC cewa sun sami saukin zirga zirga, saboda rashin bata lokaci da kuma araha, idan an kwatanta da mota ko babur.