Fursunonin siyasar Cuba na gudun hijira a Spain

Daya daga cikin iyalin fursunan siyasar Cuba da aka saki
Image caption Mutane bakwai daga cikin 'yan fursunan siyasar kasar cuba da aka saki sun fara gudun hijira a kasar spain

Gungun wasu 'yan fursunan siyasa da gwamnatin kwaminisanci ta Cuba ta saki suna kan hanyarsu na zuwa gudun hijira a kasar Spain.

An kai bakwai daga cikin su dake adawa sosai da gwamnati zuwa filin saukar jiragen sama na Havana, inda suka hadu da iyalansu, kana suka shiga jirgi suka bar kasar tare.

'Yan fursunan da aka saki dai tare da iyalansu kusan talatin zasu yi tafiya ce ta awa goma a jirgin sama zuwa kasar Spain.

Wadanda aka saki din dai suna cikin 'yan fursunan siyasa hamsin da biyu da aka saki karkashin wata yarjejeniya da aka kulla tsakanin kasar Spain da kuma Cocin Roman Katholikan kasar ta Cuba.