Sojojin Colombia sun kashe 'yan tawaye 12

Madugun 'yan tawayen Colombia, Alfonso Cano
Image caption Dakarun 'yan tawayen da ke tsaron Alfonso Cano goma sha biyu aka kashe ciki har da babbar kwamandar FARC

Sojojin kasar Colombia sun kashe akalla 'yan tawaye goma sha biyu, ciki har da wata babbar kwamanda, a ci gaba da farautar jagoran yakin sunkurun kasar da suke yi.

A wani gumurzu da suka yi da dakarun kungiyar 'yan tawaye ta FARC masu tsaron lafiyar shugaban kungiyar, Alfonso Cano, an kashe akalla sojojin na Colombia shida a wani yanki da ke kan iyakar kasar da Venezuela.

Sojojin da ke farautar Alfonso Cano dai sun gamu da turjiya ne a tsaunukan Tolima.

Bayan kura ta lafa ne sojojin suka yi aune da gawar Magally Grannobles, wadda aka fi sani da Mayerly, wadda kuma ita ce mace mafi girman mukami a kungiyar FARC.

Mayerly dai ta kwashe fiye da shekaru goma sha biyar a rundunar sojin 'yan tawayen; ita ce kuma ke jagorantar daya daga cikin sassan kungiyar FARC masu tarihi, wato 'Jaruman Marquetalia'.

Wannan sunan dai na da alaka da garin Marquetalia da ke tsaunukan Tolima, inda aka yankewa kungiyar cibiya shekaru arba'in da shida da suka wuce.

Jan dagar da 'yan tawayen suka yi dai, a maimakon su yi layar zana kamar yadda suka saba, ya nuna cewa shugabansu, wanda suke ba kariya na kusa, sun kuma yi hakan ne don su ba shi dama ya sulale.

An yi amanna cewa Shugaba Alvaro Uribe, wanda zai sauka daga mulki cikin kasa da wata guda, ya ba sojojin kasar umurni su kashe Alfonso Cano da ma hafsan hafsoshin sojojin FARC Mono Jojoy kafin wa'adinsa ya kare.