Fidel Castro ya soki manufofin gwamantin Amurka

Shugaban juyin juya halin kasar Cuba Fidel Castro
Image caption Shugaban juyin juya halin kasar Cuba Fidel Castro ya bayyana a talabijin inda a wata hira da yayi mai tsaho, indaya soki manufofin Amurka dangane da kasashen Koriya ta arewa da Iran

Shugaban juyin-juya halin kasar Cuba, Fidel Castro ya bayyana a talabijin inda yayi hirar da bai yi irin ta ba tun shekara ta 2006, yayin da ya sauka daga kan karagar mulki bisa dalilan rashin lafiya.

Shi dai Fidel Castro, dan shekaru tamanin da uku yana cikin hayyacinsa, kuma yayi bayani mai tsawo akan siyasar duniya, inda ya tabo batutuwa da dama ciki harda batun kasar Korea ta arewa da kuma kasar Iran.

Fidel Castro dai yayi bayani ne kamar yadda ya saba, inda ya soki manufofin gwamnatin Amurka dangane da kasashen Korea ta arewa da kuma Iran.