Rahoton Isra'ila ya soki hari akan jiragen ruwa na agaji

Praministan Isra'ila Benjamin Netanyahu
Image caption Praministan Isra'ila Benjamin Netanyahu

Wani bincike da rundunar sojan Isra'ila ta gudanar, kan samamen da dakarun kundumbalar ta suka kai a kan wasu ayarin jiragen ruwan Turkiyya dauke da kayan agaji, ya nuna cewa ba a yi wa matakin shirin da ya kamata ba, kuma wasu manyan hafsoshi sun tafka kurakurai.

Rahoton ya ce, akwai kuskure a bayyanan sirrin da aka samu kan aikin samamen, kana kuma babu wani shirin a zo a gani da aka yi masa.

Sai dai ana jin da wuya ne wannan sakamakon bincike ya gamsar da dayawa daga cikin masu sukar lamirin Isra'ilar.