'Kano ce kan gaba a mu'amala da kwayoyi'

Taswirar Najeriya
Image caption Jihar Kano ce gaba a jihohin Najeriya wajen mu'amala da miyagun kwayoyi, inji hukumar NDLEA

Wani rahoto da hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Nigeria (NDLEA) ta fitar ya nuna cewa jihar Kano ce kan gaba a wajen shan miyagun kwayoyi a kasar.

Hukumar dai ta yi amfani ne da alkaluman yawan masu mu'amala da miyagun kwayoyi da kuma kayan sa mayen da ta kama wajen ayyana wannan rahoton.

A wurare da dama ne dai a jihar ake cinikin kwayoyin a fili ba tare da boyewa ba, kuma matasa da dama, maza da mata, har ma da kananan yara na shiga cikin harkokin sayarwa da kuma shan kayan sa maye daban daban.

Ko da yake hukumomi suna cewa suna yin iya bakin kokarinsu wajen kawar da wannan matsala da ta addabi jihar, mazauna unguwannin da ake hada-hadar kayan sa mayen suna ganin ya kamata hukumomin su kara kaimi.

Mutanen da ke zaune a unguwannin da ake wannan hada-hada a birnin na Kano sun kuma koka da yadda lamarin ke musu barazana, musamman ga tarbiyyar 'ya'yansu.