Kungiyar Red Cross tayi kiran a agaji Niger

Matsalar yunwa a Niger
Image caption Matsalar yunwa a Niger

Kungiyar agajin Red Cross ta duniya, ta yi kira ga masu hannu da shuni da kuma gwamnatocin kasashe, da su taimaka wa kasar Nijar da kudin Euro biliyan 2 da miliyan 700, kwatankwacin CFA biliyan daya da miliyan 600, domin tinkarar matsalar yunwa a kasar.

A yanzu haka kusan rabin jama'ar Niger ne, watau mutane miliyan 7, suke fama da karancin abinci.

Kungiyar ta fitar da wannan sanarwa ce, a wani taron manema labarai da ta kira a Yamai, albarkacin ziyarar da babban sakataren kungiyar ta Red Cross, Mr Bekele Geleta, ke yi a Nijar din.