Yajin aikin ma'aikatan lafiya a jahar Kaduna

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan
Image caption A yau ne ake saran ma'aikatan kiwon lafiya a jahar kaduna dake arewacin Najeriya zasu fara wani yajin aiki.

A yau ne ma'aikatan lafiya a jihar Kaduna dake arewacin Najeriya ke fara wani yajin aiki na gama-gari, bisa abinda suka kira, rashin biya musu alkawarurrukan da gwamnatin jihar ta dauka musu na fara biyansu wani sabon tsarin albashi da kuma kyautata musu yanayin aiki.

A watannin da suka gabata dai ma'aikatan na lafiya a jihar Kaduna sun shiga yajin aiki, amma suka janye yajin aikin bayan gwamnatin jihar tayi alkawarin biya musu bukatunsu, a wancan lokacin

To amma a yanzu ma'aikatan na kukan babu daya daga cikin bukatun da aka biya musu, har yanzu kuma harkar kula da lafiya na cikin wani hali a jihar.

Jami'in dake hulda da 'yan jaridu na ma'aikatar kiwon lafiyar jahar ya shaidawa BBC cewar wasu manyan jami'an gwamantin jahar na ganawa akan wannan batu