Majalisar wakilan Faransa ta hana sanya nikabi

Wata mata da nikabi
Image caption Zai yiwu an keta 'yancin addini,"" in ji Masu kare hakki

Majalisar dokokin Faransa ta kada kuri'a domin amincewa da dokar hana mata sanya cikakken lullubin nan mai rufe fuska ruf a bainar jama'a.

A halin yanzu dokar za ta tafi gaban majalisar dattawa domin samun amincewa a cikin watan Satumba.

Wakilai 335 ne na majalisar suka kada kuri'ar goyon bayan hanin, yayin da wakili daya tak ne ya ki amincewa da shi.

Idan hanin ya zama doka, za a iya cin tarar matan da suka sanya lullubin kusan dala dari da tisiā€™in.

Hukuncin mazajen da aka samu suna tilasta wa mata sanya lullubin zai hada da kwashe shekara guda a gidan yari.

Lauyoyin kare hakkin bil adama sun bayyana cewa hanin zai iya keta hakkokin abinda jama'a suka yadda da shi da kuma na addininsu.

Rashid Nekkaz, Bafaranshe ne dan asalin Aljeriya, kuma mai fafitikar kare hakkin bil adama, sannan kuma mai kudi ta hanyar kasuwancin gidaje, ya yi tayin biyan tarar a madadin matan da za su iya fuskantar dokar a nan gaba.

Ya ce, mun yanke shawarar kafa wani asusu da zai biya tarar ga matan da suka sanya burka a kan tituna, kuma a haka zamu sa aiwatar da dokar ya zama abu mai wuya.