Mutane 2 sun hallaka a rikici a jahar Plateau

Taswirar Najeriya
Image caption Taswirar Najeriya

Hukumomin tsaro a jihar Plateau sun ce kura ta lafa a garin Federe, bayan wani rikici da ya barke.

Wasu mutane ne dauke da makamai suka kai hari a gidan hakimin garin, lamarin da ya kai ga rasuwar mutane biyu, bayan an kona gidan. Hukumomin 'yan sanda sun ce sun dukufa wajen kamo wadanda ke da hannu a lamarin.

Jihar Plateau dai ta yi ta fama da rikice rikice a 'yan shekarun nan, wadanda suka janyo asarar dimbin rayuka da dukiya.