Dan jarida ya kubce bayan an yi garkuwa da shi a Accra

Ghana
Image caption Ghana

'Yan sanda a Accra, babban birnin kasar Ghana sun sanar cewa, wani dan jarida da wasu da ba a san ko su wanene ba suka sace a jiya da marece, ya samu tserewa.

An sace Dauda Mohammed ne a lokacin da yake daukar hoton gidan da tsohon shugaban kasar, Jerry Rawlings, yake ginawa a wata unguwa dake gabashin birnin Accra.

Dan jaridar ya ce wasu mutane 3 ne, dayansu dauke da wuka, suka kama shi suka kai shi cikin wani gini, inda aka yi masa tambayoyi.

Akwai rade radin cewa masu tsaron lafiyar tsohon shugaban kasar ne, Jerry Rawlings, suka sace dan jaridar. Sai dai kakakinsa, Mr. Kofi Adams, ya musanta hakan.