Babu hanin komawa gida ga Amiri

Amiri
Image caption Ko yaushe zai koma Iran din?

Wani mai magana da yawun Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka, P J Crowley, ya ce masanin kimiyyar kasar Iran din nan, Shahram Amiri, ya je Amurka ne bisa radin kansa, don haka zai iya barin Amurkar a duk lokacin da ya so.

Kimanin shekara guda ke nan da masanin kimiyyar ya yi batan-dabo yayin da ya je aikin umra a Saudiyya.

An dai nuna shi a hotunan bidiyo guda biyu, da ra'ayoyin da suka sha bamban.

A daya yana ikirarin cewar hukumar leken asirin Amurka ta CIA ce ta sace shi, yayin daa dayan kuma yake cewa yana karatu ne a Amurkar.

Ya nemi mafaka ne a sashen da ke kula da harkokin Iran, a ofishin jakadancin Pakistan a birnin Washington, a jiya da yamma.