An azabtar da masanin kimiyyar Iran

Shahram Amiri
Image caption Shahram Amiri ya bace ne bara lokacin aikin hajji a saudi Arabiya

Masanin kimiyyar Iran Shahram Amiri ya ce hukumar leken asirin Amurka ta azabtar da shi bayan ta sace shi a Saudiyya a lokacin da ya je aikin hajji a bara.

Shahram Amiri, ya isa birnin Tehran, kuma ya musanta zargin cewa yana aikin shirin inganta makamashin nukiliya a Iran.

Mista Amiri ya ce bayan an sace shi ya fuskanci matsin lamba daga jami'an hukumar leken asirin Amurka ta CIA domin ya bada hadin kai.

"Sun azabtar da ni, har na futa cikin hayyaci na," ya kuma ce, akwai jami'an Isra'ila a lokacin da ake cin zarafin shi.

Ya kara da cewa hukumar leken asirin ta bashi dala miliyan hamsin domin ya ci gaba da zama a Amurka.

"Jami'an Amurka sun nemi na sauya sheka da son rai na, domin su samu damar cewa ina ba su bayanai game da shirin nukiliya din kasar Iran, amma da ikon Allah ban yarda da hakan ba".

Iran ta zargi Amurka

Iran ta zargi Amurka da sace masanin, zargin da Amurkan ta musanta, tana mai cewa Mista Amiri na zaune ne cikin walwala, kuma yana da damar komawa gida a koda yaushe.

Iran ta yi alkawarin baiwa mista Amiri tabbacin kula da rayuwarsa da kuma lafiyar kwakwalwarsa.

Abin da yasa wakilin BBC a Iran yace sakin nasa bai zo da sauki ba kamar yadda Iran din take nana tawa.

A ranar Talata ne dai wani mai magana da yawun Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka, P J Crowley, ya ce masanin kimiyyar kasar Iran din, Shahram Amiri, ya je Amurka ne bisa radin kansa, don haka zai iya barin Amurkar a duk lokacin da ya so.

A ranar Talata ne masanin kimiyyar nukiliyar ya nemi mafaka a ofishin jakadancin Pakistan da ke Amurka.

Mai magana da yawun ofishin kula da harkokin waje na Pakistan Abdul Basit, ya gayawa BBC cewa Shahram Amiri, na neman a gaggauta maida shi Iran. A watan Junin da ya gabata, wani ya bayyana a wasu hotunan bidiyo da ke ikirarin Amiri ne, amma sai dai bayanan sun ci karo da juna game inda yake da zama.

Amurka dai ta yi watsi da ikirarin Iran cewa ita ce ke da alhakin batan masanin kimiyyar.

A bara ne a ka sace Mista Amiri, lokacin da ya ke ziyarar aikin hajji a kasar Saudi Arabiya.

Image caption An dade ana cece kuce kan Shahram Amiri

Rade-radi

Ba a tabbatar ba ko Mista Amiri yana da wata dangantaka ta kai-tsaye da shirin bunkasa makamashin nukiliyan kasar Iran, koda yake masu sharhi na ganin cewa jami'ar da yake wa aiki na da dangantaka da batun.

Kowace irin martaba dai Mista Amiri ke da ita, bacewarsa ta jawo hasashe da kuma labarai masu cin karo da juna.

Shin ko jami'an asirin kasar Amurka ne tare da hadin bakin hukumomin Saudi Arabiya suka sace shi?

Ko kuwa dai wani yunkuri ne nasa domin tona asirin yadda kasar Iran ke bunkasa makamashin nukiliya?

Gidan talabijin na ABC a Amurka ya bada labari a watan Mayu cewa masanin ya sauya sheka inda yake taimakawa hukumar CIA da muhimman bayanai kan shirin nukiliyar Iran.

Image caption Shugaban Iran Ahmedinejad ya dade yana sa-in-sa da kasashen yamma

Amma a farkon watan nan sai Iran ta ce tana da shaidun da ke nuna cewa ana tsare da shi a Amurka.

Zargin ya zo ne bayan bayyanar wasu sakonnin bidiyo uku, inda a bidiyon farko ya ke cewa an sace shi, yayin da na biyun ke cewa yana rayuwa cikin walwala a jihar Arizona, sannan na ukun yace ya gudu daga hannun wadanda suka kama shi.

Tsohon wakilin BBC a Tehran, Jon Leyne, yace alamu na nuna cewa ikirarin na Iran na samun goyon bayan abubuwan da ke faruwa yanzu haka a birnin Washington.

Wakilin namu ya kara da cewa batan na Mista Amiri wani abin kunya ne ga hukumomin leken asirin Amurka, kuma yakan iya zama wani abun cece kuce na diplomasiyya.

A cewar Mista Basit, shugaban sashin Iran na ofishin jakadancin na Pakistan, Dakta Mustafa Rahman, na shirin mayar da masanin kimiyyar kasarsa ta asali. Sai dai duk da cewa mahukuntan Amurka ba za su iya shiga harabar ofishin jakadancin Iran ba, amma za su iya hana Mista Amir barin kasar.

'Rayuwa cikin walwala'

Sashin na Iran dai na cikin ofishin jakadancin Pakistan ne a Washington, amma Iran ce ke kula da shi. Amurka ta katse huldar diflomasiyya da Iran jim kadan bayan juyin-juya halin da aka yi a kasar a shekarar 1979.

Sakon bidiyo na kwana-kwanan ya rawaito masanin yana cewa ya gujewa jami'an tsaron Amurka.

Yayin da bidiyo biyu na farko suka bayyana harotanni masu karo da juna, wadanda aka watsa a shafin bidiyo na youTube a watan Juni.

"Ina rayuwa cikin walwala a birnin Arizona ba tare da wani tsaiko ba."

Neman dauki

A sakon bidiyo na uku, wanda gidan talabijin na Iran ya nuna a ranar 29 ga watan Juni, wani mutum da yace shi ne masanin kimiyyar yace: "Ni, Shahram Amiri, dan kasar Iran, a 'yan mintuna kadan da suka wuce na gudu daga hannun jami'an tsaron Amurka a birnin Virginia.

"A yanzu haka ina aika wannan hoton bidiyon ne cikin sirri. Za a iya sake kamani a kowanne lokaci daga yanzu."